’Yan fashin daji sun kashe mutane hudu suka yi garkuwa da wasu 150, ciki har da jarirai a a wani kauye da ke Karamar Hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara.
A ranar Lahadi ne ’yan fashin dajin suka kai harin inda suka yi wannan aika-aika a kauyen Dan Isa da ke da tazarar kilomita 14 daga Gusau, babban birnin jihar.
’Yan fashin dajin sun yi wannan danyen aiki a Dan Isa ne kimanin mako guda da suka sako mutane 46 da suka sace a kauyen Dogon Kade bayan karbar kudin fansa Naira miliyan 21.
Wani magidanci a kauyen Dan Isa ya tabbatar wa Aminiya cewa ’yan fashin dajin sun yi awon gaba da matarsa a yayin harin da suka shafe kimanin awa shida suna cin karensu babu babbaka, tun daga misalin karfe uku na ranar Lahadi.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Azumin Tasu’a Da Ashura
- ‘’Yan bindiga sun sa mana harajin N200m’
Ya bayyana cewa ’yan fashin daji sun zo ne a kan babura kimanin 150 kowanne da mutane uku a kansa, suna harbi kan mai uwa da wabi.
“Mai dakina Na’ima da jaririnmu dan wata shida mai suna Sudais suna daga cikin wadanda aka tafi da su.
“An kuma tafi da matar dan uwana da jaririnta dan wata takwas, da kuma wasu mata da kananan yara da dama,” in ji magidancin.
Wani mazaunin kauyen Dan Isa na daban, ya bayyana cewa Hajiya Rakiya, matar Wamban Dan Isa, Alhaji Bello Halilu, tana daga cikin wadanda ’yan bindigar suka yi garkuwa da su.
Ya kara da cewa akwai wasu matan kuma da ’yan fashin dajin suka yi wa rauni a gidan Wambai Alhaji Bello Halilu
Ita ma Malama Luba da Malama Talatu, matan kanin wamban suna daga cikin wadanda aka yi awon gaba da su a harin.
Ya ci gaba da cewa “Na samu labarin cewa Malam Musa Ajiya yana cikin mutanen da suka tsere daga hannun ’yan bindigar, amma an tafi da ’yan gidansa hudu, ciki har da matarsa Suwaiba da matar kaninsa Shafi’u.”
Shi kuma wani dan garin mai suna Aminu Bello Dan Isa, ya shaida mana cewa yaran kasurgumin dan fashin daji, Alhaji Shehu Bagiwa, ne suka kai harin.
Duk da cewa shaidu sun ce ba da Bagiwa aka kai harin ba, amma sun bayyana cewa matan da suka tsere sun ce sun ga mataimakinsa, Aminu Baka-da-dadi, yana jagorantar ’yan bindigar.
“Wasu mata da suka tsere sun dawo da karaya a kafafunsu da raunuka a jikinsu sakamakon dukan da ’yan bindigar suka yi musu a cikin daji,” a cewar Aminu Dan Isa.
Aminiya ta gano cewa harin ya sa mazauna kauyen yin kaura zuwa wurare irin su Kasuwar Daji, Rawayya, Gyambarawa, da kuma Gusau, saboda tsoron dawowar maharan.
Kauyen Dan Isa ya shafe kusan shekaru biyar yana fuskantar hari daga ’yan bindiga da suka hallaka rayuka tare da yin garkuwa da mutane da dama.
Sakamakon haka mazauna suke rokon gwamnati ta girke sojoji a garin kuma ta kawar da ’yan ta’adda musamman irin su Bagiwa da Baka-da-dadi.
Aminu Bello ya ce, “Muna bukatar a kawo mana karin jami’an tsaro, in ba haka ba, ba za mu koma ba.”
Ya ce, “Da can akwai sojoji a kauyen, amma da aka dauke su zuwa wani wuri sai ’yan fashin daji suka dawo da kawo mana hari kusan duk lokacin da suka ga dama.
“’Yan bindigar ba su da imani, tabbas idan aka hallaka su komai zai daidaita za a samu sauki a nan yankin, saboda su ne matsalarmu a nan da ma sauran sassan jihar.”
Ba mu da labarin —’Yan sanda
Mun tuntubi Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Zamfara Muhammad Shehu Dalijan, amma ya ce rundunar ba ta samu rahoto game da harin na Dan Isa ba.
Amma ya tabbatar da wani da aka kashe mutane biyar aka sace wasu 11 a Gusau a makon jiya.
Ya bayyana cewa ’yan sanda sun dakile wani hari a yankin Damba da ke wajen garin Gusau, inda suka yi nasarar kashe wasu daga cikin ’yan bindigar.
Ya bayyana cewa rundunar ta kara tsaurara matakan tsaro a Gusau inda ta girke motocin sintiri huda 54.
Ta kuma roki al’umma da su rika taimaka wa jami’an tsaro da bayanai domin yakar ayyukan ta’addanci.
Karuwar hare-hare a Zamfara
A baya-bayan nan ’yan bindiga sun yawaita kai hare-hare a sassan Jihar Zamfara.
Aminiya ta ruwaito yadda ’yan fashin daji suka sace mutane a yankunan Karamar Hukumar Zurmi.
’Yan bindigar sun kuma lafta wa wasu yankunan harajin kudi kusan Naira miliyan 150 a matsayin sharadin barin mazauna su noma gonakinsu.
Wasu daga cikin kauyukan sun biya nasu harajin a yayin da wasu ke fadi-tashin hada kudaden kasancewar a wannan mako wa’adin biyan harajin ke cika.
Kauyuka da abin ya shafa su ne:
Yan Dolen Kaura, miliyan N15; Gidan Zagi, miliyan N15; Kanwa, miliyan N20; Kaiwa Lamba, miliyan N26; Gidan Dan Zara, miliyan N22; Jinkirawa, miliyan N16; Dumfawa, miliyan N16 million; Ruguje, miliyan N7; Babani, miliyan N3 sai Gidan Duwa, miliyan N4.