✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan fashi sun kai wa tsohon wakilin Daily Trust hari a Neja

'Yan fashin sun kai masa hari da misalin ƙarfe 2 na dare a gidansa da ke Minna.

Wasu da ake zargin ’yan fashi da makami ne, sun kai wa tsohon wakilin jaridar Daily Trust, Aliyu Hamagan hari a gidansa da ke Minna a Jihar Neja.

Ɗan jaridar ya fake a gidan wani abokinsa, inda ya shaida wa Aminiya cewa ’yan fashin sun shiga gidansa ne da misalin ƙarfe 2 na dare.

Ya bayyana cewar suka kai masa hari da wuƙaƙe da gatari wanda hakan ya kai ga kwantar da shi a Babban Asibitin Minna.

Ya ce maharan sun tafi da kwamfyuta ɗinsa, iPad, iPhone, ƙaramar waya, da dai sauran kayayyaki.

Hamagan, ya ce maharan sun yi barazanar kashe shi idan ya yi wani yunƙuri tona musu asiri.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce ba shi da masaniya kan faruwar lamarin.