✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan fashi sun harbe mai yi wa kasa hidima

’Yan fashi sun yi wa motar masu yi wa kasa hidima ruwan wuta

Wani matashi mai yi wa kasa hidima ya bakunci lahira bayan ’yan fashi sun yi musu ruwan wuta a kan babbar hanyar Jere zuwa Abuja.

Hukumar Kula da Masu Yi wa Kasa Hidima (NYSC) ta ce Bomoi Suleiman Yusuf ya rasu ne bayan ’yan fashin sun bi tare da yin ruwan harsasai babu kakkautawa a kan motar da masu yi wa kasa hidima 17 suka hau zuwa Arewacin Najeriya bayan kammala samun horo a sansaninta da ke Jihar Osun.

“Mutuwar mai yi wa kasa hidima babban rashi ne ba ga iyalansa ba kadai, har ga shirin NYSC da ma kasa baki daya”, inji Daraktar Yada Labaran hukumar, Adenike Adeyemi.

A sakon ta’aziyyar hukumar ga iyalan matashin, Adenike ta yi karin haske cewa ragowar matasan NYSC 16 da ke cikin motar sun tsallake rijiya da baya sabanin jita-jitar da ke cewa an yi gakwa da su ba.

Ta yi addu’ar samun rahama ga Bomoi Suleiman Yusuf tare da “tunatar da masu yi wa kasa hidima da su rika bin dokokin kariyar hukumar wadda ke kyamatar yin tafiye-tafiye da dare.”