Wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan fashi ne, sun kai hari fadar Sarkin Minna da ke Jihar Neja, Alhaji Umar Farouk Bahago, inda suka kashe Dogarai biyu.
Rahotanni sun ce maharan wadanda yawansu ya kai biyar sun kai farmakin ne ranar Talata, wajen misalin karfe 4:00 na La’asar.
- Dan takarar Gwamna ya je kotun sauraron kararrakin zabe da shaidu 8,000
- Gwamnatin Taliban ta ba da umarnin rufe dukkan shagunan gyaran jiki a Afghanistan
Wakilinmu ya gano cewa Sarkin na Minna na cikin fadar lokacin da ’yan fashin suka rika harbi a sama domin tarwatsa jama’a, kafin daga bisani su yi awon gaba da wasu kudade mallakin masarautar.
Tuni dai aka kai biyu daga cikin Dogaran da aka jikkata zuwa babban asibitin Minna domin samun kulawar likitoci.
Aminiya ta kuma gano cewa maharan sun biyo sahun wani dogari ne da aka aika banki, inda suka biyo shi a kan wata mota har cikin fadar.
Wani makwabcin fadar da bai amince a ambaci sunansa ba ya shaida mana cewa an yi ta fafatawa tsakanin jami’an tsaron fadar da ’yan fashin, kafin daga bisani a fi karfin jami’an tsaron.
Sai dai duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Wasiu Abiodun, kan lamarin ya ci tura saboda rashin amsa kiran wayar wakilinmu ko amsa rabutaccen sakon da aka aike masa, har zuwa lokacin hada wannan rahoton.