Wasu gungun ’yan fashi da makami sun kai hari Unguwar Sabon Gari da ke kan hanyar garin Cakwaya na Karamar Hukumar Rano ta Jihar Kano.
Wani ma’abocin shafin sada zumunta na Facebook ne ya bayyana wannan fargaba yayin da wallafa sakon cewa ’yan fashi da makamin sun afka gidajen mutane a karshen makon da ya gabata.
- Kotu ta umarci Sarkin Dubai ya biya tsohuwar matarsa Dala miliyan 500
- Kungiyoyin kwallon kafa 15 da suka sallami masu horaswa a Turai
Hakan dai na zuwa ne sakamakon razanar da aka yi na cewa ana zaton gungun ’yan fashi da makamin ’yan bindiga ne, la’akari da yadda kwanaki kadan da suka gabata rahotanni suka bayyana cewa ’yan bindigar da suka kai hare-hare a wasu yankunan Jihar Kaduna na shiga Jihar Kano.
Sai dai wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa Aminiya cewa, lamarin ya faru ne da misalign karfe 1.00 na daren ranar Lahadi, inda gungun ’yan fashi da makamin suka ci karensu babu babbaka har zuwa karfe 4.00 ba tare da fuskantar wata tirjiya ba.
A cewarsa, sun kai hari ne gidan wani dan kasuwa mai suna Auwalu Rabi’u mai sayar da wayoyin salula da kayan masarufi a babbar kasuwar garin.
“Gungun ’yan fashin sun haura mutum 20 kuma kai tsaye suka zarce gidan mutumin, inda suka yi ta kwankwasa kofar gidansa amma ya ki bude musu.
“Daga bisani an samu wani da ya ankarar da ’yan sanda kuma nan take suka iso, wanda hakan ya sanya ’yan fashin suka ranta a na kare.
Auwalu Rabi’u, mutumin da ’yan fashin suka kai hari gidansa, ya ce koda yake bai samu ya yi ido biyu da sub a, amma ya tabbatar cewa suna da yawan gaske kuma kowanensu dauke da muggan makamai.
Ya ce, “sun yi ta bugun kofar gidana amma na ki budewa, daga baya suka balle kofar, amma suka kasa bude wata kofar da suka sake yin arba da ita wadda ita ce za ta ba su damar shiga gidan.
“Sun shafe kusan minti 20 suna kwankwasa kofar, amma yayin da suka ji alamun zuwan ’yan sanda sai suka tsere,” a cewar Auwalu.
“Babu wani sako da suka bari, amma dai sai da suka bincike ko’ina a harabar gidan sannan suka kama gabansu.
Wata majiya daga fadar Sarkin Rano ta ce ta samu labara a kan lamarin, kuma tuni Sarkin ya umarci rundunar ’yan sandan da ke yankin da ta binciki lamarin.
Sai dai har ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, Kakakin ‘yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa da wakilinmu ya tuntuba bai ce uffan a kan lamarin ba.