✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yan Daba Sun Kashe ’Yan Sanda a Kogi

Wasu bata-gari da ake zargin ’yan daba ne, sun halaka ’yan sanda biyu a titin Agbaja da ke Lokoja, babban birnin Jihar Kogi.

Wasu bata-gari da ake zargin ’yan daba ne, sun halaka ’yan sanda biyu a titin Agbaja da ke Lokoja, babban birnin Jihar Kogi.

Rahotanni na nuna ’yan daban sun far wa jami’an ne lokacin da suka je sintiri unguwar Agbajan ranar Laraba, suka bude musu wuta, har suka harbe ’yan sandan biyu, sannan suka tsere daji.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar SP William Aya, ya ce bincikensu ya nuna daga cikin daji ’yan daban suka fito, suka far wa ’yan sandan.

Ya ce rundunar ta umarci mataimakin kwamishinan ’yan sandan jihar ya bincika lamarin, domin lalubo wadanda suka yi ta’asar su girbi abin da suka shuka.