Wasu matasa da ake kyautata zaton ’yan daba ne sun yi kwanton bauna tare da kai wa Shugaban Jami’ar Obafemi Awolowo (OAU) da ke Ile-Ife, Farfesa Eyitope Ogunbodede, hari a cikin makarantar.
’Yan dabar dai na dauke ne da muggan makamai da suka hada da bindigogin l da adduna yayin harin, kuma sun hana Shugaban da wasu manyan jami’an makarantar shiga wasu sassa nata.
- Fitattun jaruman da rasuwarsu ta girgiza Kannywood a 2021
- Kaduna: ’Yan bindiga sun harbe basarake a Giwa, kwana 1 bayan kashe mutum 38
Matasan, wanda ake zargin harin nasu na da nasaba da rikicin wasu filaye, sun rika fito da makaman tare da yin harbi kan mai uwa da wabi da bindigoginsu.
Sun kuma kai wa Kakakin jami’ar, Mista Abiodun Olanrewaju, tare da sauran ’yan jarida hari, suna barazanar kashe su.
Rahotanni sun ce ana zargin wasu masu rigimar filaye da hukumar makarantar ne suka dauko hayar ’yan dabar don hana su shiga wasu sassa nata.
Shugaban jami’ar dai ya yi Allah wadai da harin, inda ya ce ko taku daya makarantar ba za ta bari ba.
Farfesa Eyitope ya ce sakamakon barazanar da mutanen suke yi wa daliban, sun kasa komawa sabon ginin dakunan kwanan daliban da aka yi a kan filin da ake rigima a kai.
Ya ce, “Ba na son mu rasa ran kowane dalibi. Muna fama da matsalar dakunan kwanan dalibai, amma hakan ba ya nufin za mu yi wasa da rayuwarsu.
“Kun dai ga abin da ya faru yau, Allah ne kawai ya tsallakar da mu, amma za mu ci gaba da tattaunawa da wadannan yankunan,” inji shi.