Masu garkuwa da suka yi awon gaba da mutum 20 a jihar Kaduna na neman kudin fansa Naira milian 900 kafin su sako mutanen.
Dangin wata mai abinci da ’yan bindigar suka yi garkuwa da ita sun ce mutanen sun yi barazanar “mayar da ita matarsu” idan ba a ba su kudin fansa Naira miliyan 200 ba a kanta.
Kawun budurwar ’yar shekara 19 ya ce “Masu garkuwar sun kira ranar Litinin da yamma suna neman kudin fansa Naira miliyan 200, suka kuma kara kira ranar Talata da rana suna tambaya ko kudin sun samu. Mahaifinta direban babur mai kafa uku ne kuma ba na shi ba ne”.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto, wakilinmu ya yi kokarin tuntubar Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, domin jin inda aka kwana, amma bai same shi.
Kazalika Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Mohammed Jagile bai dauki kiran da ya yi masa a waya ba.
A dare Lahadi 12 ga watan Yuli ne ’yan bindiga sanye da kayan jami’an tsaro suka kafa shingen bincike inda suka kashe mutum biyu suka kuma yi garkuwa da wasu 20, a unguwar Dambushiya da ke yankin Sabuwar Kaduna a Karamar Hukumar Chikun.
“Sun zo sanye da kayan sojoji da ’yan sanda suka kafa shingen binciken ababen hawa a daidai gadar shiga unguwar, suka yi ta tsayar da masu ababen hawa”, inji wani mazaunin yankin.
Ya ce direbobi da yawa sun tsaya domin sun zaci jami’an tsaro ne, amma da wani mai shagon ya yi kokarin tserewa da ya yi zargin cewa ’yan fashi ne sai suka harbe shi.
“Sun kuma kashe wani karin mutum daya”, inji shi.
Mazauna yankin sun ce ’yan fashin sun sa shingen binciken nasu ne a kusa da gabar shiga yankin Sabuwar Kaduna, da misalin 8.00 na daren Lahadi.