✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindigar da ke addabar mu ’yan kabilar Ibo ne —Gwamnan Anambra

Gwamnan Anambra Farfesa Charles Soludo ya ce daukacin ’yan bindigar da dubunsu ta cika a jihar ’yan kabilar Ibo ne.

Gwamnan Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya ce ’yan bindigar da ke addabar jihar ’yan kabilar Ibo ne, ba daga wani wuri suka shigo ba.

Soludo ya bayyana cewa kawo yanzu, “Daukacin ’yan bindigar da ke tsare a hannunmu ’yan kabilar Ibo ne, ba masu kutse daga wani wuri ba kamar yadda ake yada ji-ta-ji-ta.

Ya ce, “Bari in fada karara, duk wadanda muka kama ’yan kabilar Ibo ne, babu wasu masu mamaya daga wani wuri — Tsantsar ’yan kabilar Ibo ne ke wa ’yan uwansu wannan abu.”

Da yake sanar da haka a hirar da shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin na Channels ya yi da shi, gwamnan ya ce, “Masu aikata manyan laifuka ne kuma wadansu daga cikinsu suna fakewa da sunan fafutikar kungiyar IPOB.”

Amma ya bayyana cewa, haramtacciyar “Kungiyar ta sha nesanta kanta da masu yin wadannan abubuwa.”

Gwamnan, wanda ya ce gwamnatinsa ta dauki matakai domin magance mastalar, ya bayyana cewa ’yan bindigar, “Masu garkuwa da mutane ne domin karbar kudin fansa.”

Ya ci gaba da cewa, “Wadanda muka fara kamawa ’yan kabilar Ibo ne da suka shigo Anambra daga wasu jihohin yankin Kudu maso Yamma.

“Amma da muka zurfafa bincike sai muka gano cewa akwai matasanmu masu yawan gaske da suka shiga cikin wannan mummunar harka.”

Ya bayyana cewa Anambra ta tsinci kanta a wannan yanayin ne saboda yawan masu zuwa daga wasu jihohin Kudu maso Gabas domin neman kudi a jihar.

Ya ci da cewa “Suna kuma yin wannan kazamar harka ce saboda ganin cewa ana samun kudi da ita.

“Babu shakka Anambra ce jiha mafi arziki a yankin Kudu maso Gabas; shi ya sa ’yan bindigar suka tare a nan suke sace mutane fiye da a sauran jihohin yankin.

“Amma muna murkushe su; Babu wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba.

“Watakila wadanda ba a sani ba su ne wadanda dubunsu ba ta riga ta cika ba.

“Amma ina tabbatar maka cewa mun kama da yawa daga cikinsu, kuma yanzu sun san cewa Anambra ba maboyarsu ba ce.”

A cewarsa kawo yanzu, matakan tsaro da gwamnatinsa ta dauka sun kawo aminci, jama’ar jihar kuma shaida ne a kan haka.