Ministan Tsaro na Najeriya Bashir Magashi ya ce yaki da ‘yan bindiga a sassan kasar ba abu ne da ya takaita a kan sojoji ba kadai.
A jawabinsa na Ranar Rundunar Sojin Kasa ta 2020 a babban sansanin soji da ke Faskari jihar Katsina, Magashi ya ce duk da haka ana kara samar wa rundunar sojin Najeriya kayan aiki domin magance matsalolin tsaro.
“Yakar matsalar tsaro aiki ne na hadin gwiwa ba na sojoji kadai ba, kowane dan kasa na gari na da rawar takawa wajen kawo karshen matsalar, kuma ya kamata kowa ya bayar da gudunmuwa ta wannan fuska”, inji Magashi.
A nasa jawabin, Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce a cikin shekara biyar da suka wuce rundunar ta yi kokari matuka wajen biyan bukatun dakarunta na mayaka da kayan aiki.
A cewarsa, an samu karuwar barazanar tsaro a duniya da ma Najeriya mai fama da rikicin kungiyar Boko Haram, ‘yan bindiga da masu garkuwa.
Sai dai ya ce matsalar Boko Haram ta ragu yanzu, idan aka kwatanta da shekara biyar da suka gabata.
Buratai ya kuma mika godiyar rundunar ga Shugaba Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo da majalisun tarayya da ministan tsaron game da yadda suka bayar da dage wajen ganin rundunar na samun biyan bukata domin gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.