Fitaccen malamin nan na addinin Islama da ke Jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce ’yan daban daji da aka fi sani da ’yan bindiga suna aikata ta’addanci amma a hakikanin gaskiya ba ’yan ta’adda ba ne.
Bajimin malamin ya yi wannan furuci ne a wata tattaunawarsa da Aminiya, gabanin Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta ayyana ’yan bindiga ko kuma ’yan daban daji a matsayin ’yan ta’adda.
A cewarsa, kiraye-kirayen da ake ta yi wa gwamnati domin ta ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda ya samo asali ne daga salsala ta son zuciya da bangaranci.
“Babban abin takaicin shi ne don zuciya ne yake jawo hakan. IPOB alal misali kungiya ce, amma ba ta wakiltar duk ’yan kabilar Ibo. Boko Haram kungiya ce, amma ba ta wakiltar ’yan kabilar Kanuri.
“Saboda haka ana iya ayyana ’yan Boko Haram a matsayin ’yan ta’adda, kuma ana iya ayyana IPOB a matsayin kungiyar ta’adda.
“Amma a wannan lamari, su wa aka ayyana a matsayin’yan ta’adda?
“Furta kalmar ’yan bindiga ko ’yan daban daji wani kwatance ne marar gamsasshiyar ma’ana, to me kuma za a ayyana?
Ko so ake a ce Makiyaya ’yan ta’adda ne, wannan shi ne. Su ’yan awaren Biyafara na IPOB da aka ayyana cewa ’yan ta’adda ne, wane tasiri hakan ya haifar ko akwai wani zani da hakan ya sauya?
“Amurka, Kungiyar Tarayya Turai da ko’ina a fadin duniya ba su amince da wannan ayyanawa da aka yi ba.
“Ba su sanya musu takunkumi ba ko sun dauki wani mataki a kansu, sannan ba su hana su tafiye-tafiye ba.
“Har yanzu suna samun gudunmuwar kudi, kila ko don kusanci ko alakar da ke tsaninsu da su ta fi wacce take tsakaninmu da su karfi.
“Saboda haka a kan wannan gaba, idan aka ce Fulani makiyaya ’yan bindiga ne kalmomi ne kawai aka fada, amma ba za a iya kiran ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda ba.
“Eh, tabbas suna aikata ta’addanci amma ba a ’yan ta’adda ba ne.
A bayan nan ne Sheikh Gumi ya ce ayyana ’yan bindiga a matsayin ’yan ta’adda abu ne mai hatsari, lamarin da ya ce da zarar hakan ta tabbata, kungiyoyi masu ikrarin jihar na ketare kai tsaye za su fara taimaka musu da daukar nauyinsu a bangaren kudi.