Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan awaren Biyafara ne, sun ƙone wani gidan mai na kamfanin Pinnacle da ke Jihar Enugu.
Lamarin wanda ya faru da misalin ƙarfe 10 na safiyar Juma’a a kan titin Agbani, ya sanya wasu motoci huɗu ƙone da ke harabar gidan man.
- A tabbatar an mutunta tsarin dimokuraɗiyya a Zaɓen Edo — Tinubu
- An tsinci gawa a rataye cikin makarantar Islamiyya a Jigawa
Majiyar Jaridar The Nation da ta ziyarci wurin da lamarin ya faru, ta gano cewa ‘yan bindigar da suka kai mutum huɗu, sun kawo harin ne a wata mota ƙirar Toyota Corolla.
Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun ƙwace kan famfunan man ne daga hannun ma’aikatan masu sayarwa, inda suka rika yi wa motocin da ke kusa feshi da famfon sannan suka banka musu wuta.
Haka kuma, ‘yan bindigar sun kone wasu motoci uku da ke wajen wankin mota a cikin harabar gidan man.
Jami’an hukumar kashe gobara ta Jihar Enugu da na Hukumar Agajin Gaggawa, su ma an gansu suna fafatukar kashe gobarar yayin da kwamishinan ‘yan sandan jihar ya jagoranci tawagarsa domin tantance irin ɓarnar da lamarin ya haddasa.
An ce lamarin ya haifar da firgici a yankin, inda ya tilasta wa ‘yan kasuwa da mazaunan da ke kusa suka rufe harkokinsu.
‘Yan sandan sun kuma killace titin Agbani, inda suka tilasta wa masu ababen hawa yin amfani da wasu hanyoyin ta Emeka Ebola zuwa Amokwe da Uwani zuwa Tashoshin Bus na Nise.