’Yan bindiga sun yi wa mutum uku yankan rago sannan sun sace wasu da dama a kauyen Maguzawa da ke Karamar Hukumar Rafi da ke Jihar Neja.
Majiyoyi da dama sun rawaito cewa cikin wadanda aka yi garkuwa da su akwai mata da kananan yara, yayin da wasu mazauna unguwar suka tsere zuwa Pandagori, da kuma Birnin Gwarin Jihar Kaduna.
- Cutar Kyandar Biri ta kama mutum 2 a Filato
- NUC ta sabunta wa darusa 12 lasisin karatu a jami’ar Maitama Sule
Garin Maguzawa dai na da nisan kilomita 25 daga birnin Kagara da ke Neja, yayin da daga Birnin Gwarin ta ke da kilomita 12.
Harin garin Maguzawan na zuwa ne kasa da kwana biyu bayan ’yan bindiga sun far wa kauyen Gidigore da ke Karamar Hukumar Rafi a daren Talata, inda aka samu mutuwar mutane biyar da satar wasu da dama.
Wasu mazauna yankin sun bayyana wa wakilinmu cewa kauyuka da dama da ke Rafin na fuskantar hare-haren ’yan bindiga tsawon sati ukun da suka gabata.
“Kasa da sati uku ke nan da aka kawo mana hare-haren 10 a kauyuka daban-daban da ke Karamar Hukumar Rafi. kusan kullum haka muke,” inji wani mazaunin yankin.
Wani ganau, Ibrahim Ahmad, wanda dan uwansa na daga cikin wadanda aka sacen daren Talata ya ce mutane da dama sun yi kaura daga kauyen.
“Kafin ma harin na ranar Talata, sati biyu da suka wuce ’yan bindiga sun kai hari Gulbi, Unguwan-Jaye da Kusherki suka kashe mutane takwas, suka kuma sace mutane 36.
“Bayan haka kuma sun raunata mutum guda, yanzu maganar da nake maka ma sun ce sai an biya Naira miliyan 59 kafin su saki mutanen da suka sace da fari,” inji shi.
Kakakin Rundunar ’Yan sandar Jihar, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a Didigore amma bai ce komai ba kan na baya-bayan nan.
Haka kuma ya ce yayin harin, kusan mutane uku ne suka rasu, sai kuma wani adadi da ba tantance ba na wadanda aka sace, tare da kona gidaje biyu.