Akalla mutum hudu ne aka kashe, ciki har da wani hakimi da aka yi wa yankan rago, yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai garin Tunga Rafin da ke Karamar Hukumar Augie a Jihar Kebbi a daren Laraba.
An rawaito ‘yan bindigar da yawansu ya haura 70 ne suka kai farmaki kauyen cikin dare, inda suka kashe Hakimin yankin mai suna Abubakar Magaji (Sabo Rafi) da wani mutum guda.
- Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 44 a Arewacin Najeriya
- Mutum 2 sun gurfana a gaban kotu kan zargin bata sunan Ganduje a wasan barkwanci
Wani mazaunin kauyen da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da mata da yaron Hakimin bayan sun yi masa yankan rago.
Ya ce ‘yan bindigar sun kuma kashe wasu mutum biyu da suka ci karo da su a hanya yayin da suke ficewa daga kauyen.
“Sun gudu lokacin da suka fahimci mutanenmu suna kokarin kai musu hari,” inji shi.
Ya ce wannan ne karon farko da ‘yan bindiga suka kai hari kauyen duk da cewar suna farmakar makwabtansu.
“Ba mu san za su kai mana hari nan kusa ba, duk da cewa sun sha kai hari ga wasu yankunan.
“Mutane da yawa sun fito domin dakile harin da suka kai wa al’umma amma sai suka kashe shugaban kauyenmu da wasu mutum uku sannan suka gudu,” in ji shi.
Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar, SP Nafiu Abubakar, ya ce har yanzu ba su tabbatar da faruwar lamarin ba.
Sai dai ya yi alkawarin yin karin haske da zarar ya samu wani bayani.