’Yan bindiga sun kai farmaki a kauyen Gamji da ke Karamar Hukumar Bakura ta Jihar Zamfara, inda suka yi awon gaba da ’ya’ya biyu na tsohon Kwamishinan Kananan Hukomomi da Masaratu na jihar, Muhammad Bello Dankande Gamji.
Mahaifin yaran da abin ya shafa yayin zantawa da wakilanmu ya ba da tabbacin cewa ’yan bindigar sun kuma harbe wani mutum daya a gidan nasa.
Ya kuma ce sun yi garkuwa da wani jami’in Hukumar Tsaron Cikin Gida (NSCDC) da ya kasance dogari a gidansa da kuma wani makwabcinsa guda daya.
Mai Magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantawa da manema labarai.