Kimanin mutum 19 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Ogu da Tegina da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.
Ogu yanki ne da ke kusa da Wayam kimanin kilomita biyu daga Kagara, hedikwatar Karamar Hukumar Rafi.
- ‘Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da 5 a Neja
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum 20 a Neja
- ‘Yan bindiga sun kai hari kasuwanni, sun kashe mutane 4 a Neja
- Gobarar tankar mai ta hallaka mutum biyar a Neja
Wani mai suna Kamal Mamman Wayam a yankin Ogu da ya gane wa indonsa faruwar lamarin ya ce: “’Yan bindigar sun shigo yankin suna ta harbi a iska, suka dinga awon gaba da dukiyoyin mutane, tare da garkuwa da mutum shida nan take”.
Ya ce ’yan bindigar sun afka wa Ogu ne da safiyar Lahadi kuma suka fara harbi a sama.
Shi kuwa harin da aka kai wa Tegina an ce ya faru ne da misalin karfe 12:30 na daren Litinin.
Wani mazaunin yankin, Sani Gamachindo wanda wakilinmu ya tattauna da shi ta wayar tarho, ya ce an yi garkuwa da mutum 13.
“’Yan bindigar sun shiga gidan diyata, amma Allah Ya taimaka ta buya a karkashin gado, mai gidanta kuma ya buya a cikin rufin daki; da suka shiga sai da suka cinye abincin da suka tarar a dakin”, inji Gamachindo.
Mahara sun yi barna a yankin Rafi
Harin ’yan bindigar na zuwa ne kwana hudu bayan sace Shugaban Matasan jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Rafi, tare da garkuwa da Hakimin Gunna da wasu ma’aikatan lafiya biyu a yankin Garin Gabas da Yakila.
A ranar Juma’ar da ta gabata, ’yan bindiga sun rufe babbar hanyar da ke tsakanin Zungeru da Tegina na tsawon awanni, inda suka dinga harbe-harbe ba kakkautawa.
Da wakilinmu ya tuntubi kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja, ASP Wasiu Abiodun, don jin ta bakinsa, sai ya ce zai nemi wakilin namu wanda har yanzu hakan ba ta samu ba.
’Yan bindiga sun kashe Fasto a Shiroro
A wani labari makamancin wannan kuma, ’yan bindiga sun kashe wani Fasto a cocin Evangelical Church Winning All, ECWA a Chukuba, Karamar Hukumar Shiroro da ke jihar.
Wani babban jami’i a cocin ECWA Goodnews da ke Minna, ya ce Fasto Ibrahim ya tafi duba gonarsa ne da ke Chukuba tare da ziyartar wani abokin aikinsa wanda Fasto ne na Chukuba, inda a nan ne ’yan bindigar suka farmake shi har suka kasha shi.