✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake a Zamfara

Mahara sun yi awon gaba da Mai Garin Lingyado da wasu mutum hudu a Zamfara

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Mai Garin Lingyado tare da mutane hudu a Karamar Hukumar Maru da ke Jihar Zamfara.

Hakan ya fito ne cikin wani jawabi da Kakakin Rundunar ’Yan sandan jihar Mohammed Shehu ya fitar.

“Ranar 25 ga watan Oktoba ’yan bindiga sun yi garkuwa da mai gari tare da mutum hudu a kauyen Lingyado.

“Hadin gwiwar ’yan sanda da sojoji sun kai dauki kauyen bayan mun samu kiran gaggawa daga wata lambar waya”, a cewar Shehu.

Ya kara da cewa sun baza jami’an tsaro a dukkanin dazukan da ke makwabta da kauyen domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su taimaka wa ’yan sandan da duk wani bayani game da wani abu da ba su yarda da shi ba.