Wasu ’yan bindiga da yawansu ya kai kusan 10 sun mamaye masarautar Mbutu da ke Karamar Hukumar Aboh Mbaise ta Jihar Imo, inda suka yi awon gaba da basarakenta, Eze Damian Nwaigwe.
An dai sace shi ne a fadarsa, wajen misalin karfe 2:30 na daren ranar Alhamis, kamar yadda wata majiya a yankin da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa wakilinmu.
- Sabuwar doka ta ba ’yan New Zealand damar sauya jinsinsu na haihuwa
- Tirelar da jami’an Kwastam ke kokarin kamawa ta danne mutum 4 a Kwara
A cewar majiyar, “An sace basaraken masarautar Mbutu da ke Karamar Hukumar Aboh Mbaise ta Jihar Imo, Eze Damian Nwaigwe, da sanyin safiyar nan.
“’Yan bindigar da suka zo suka tafi da shi suna da yawa sosai.
“Sun zo ne a kan mota, kuma sun kai su 10, sannan suka yi wa fadarsa kawanya, suka yi ta harbi a iska, kafin daga bisani su wuce da shi a cikin motar,” inji majiyar.
Rahotanni dai sun ce fadar dai ba a tsakiyar gari take ba, lamarin da ya sa mutane ba su iya zuwa don kawo dauki ba.
Kakakin ’Yan Sandan Jihar, CSP Mike Abattam, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya kuma ce tuni rundunar ta bazama wajen ganin ta ceto basaraken ba tare da an cutar da shi ba.