’Yan bindigar da suka sace mutum 17 a Kauyen Kawu da ke Karamar Hukumar Bwari a babban birnin tarayya, Abuja sun yi barazanar kashe sauran mutum 11 da ke hannunsu kan rashin biyan kudin fansa a kan lokaci.
Aminiya ta ruwaito yadda ‘yan bindigar suka kai farmaki kauyen a ranar 11 ga watan Janairu, 2024, inda suka yi awon gaba da mutum 18.
- Yadda Tsadar Rayuwa Ta Sa Aka Koma Hawa Jaki A Arewa, Kudu Kuma Tafiyar Ƙafa
- Nijar, Mali da Burkina Faso sun fice daga ECOWAS
Daga cikin wadanda maharan suka sace, ciki har da mata da miji, ɗan hakimin kauyen da kuma wata ma’aikaciyar jinya.
Sai dai a ranar Litinin, 22 ga watan Janairu, 2024, ‘yan bindigar sun sako mutum hudu bayan biyan su miliyan biyar, inda suka ci gaba da tsare mutum 11.
Daya daga cikin ‘yan uwan wadanda aka sace, Bala Danjuma, ya ce shugaban ‘yan bindigar ya kira su da safiyar ranar Asabar tare da yin barazanar kashe sauran mutum 11 da ke hannunsu sakamakon gaza biyan kudin fansa a kan lokaci.
Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Adeh Josephine, ba ta ce komai kan sakon da aka aike mata ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.