Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi awon gaba da shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) reshen jihar Taraba, Peter Jediel.
An sace shi ne da misalin karfe 1:12 na daren ranar Lahadi daga gidansa dake Sunkani, shalkwatar Karamar Hukumar Ardo-Kola ta jihar.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar, wadanda yawansu ya kai kusan 12 sun rika harbi kan mai uwa da wabi domin su tsorata mutanen dake da makwabtaka da gidansa, kafin daga bisani su dauke shi su tafi da shi.
Wani dan uwa ga shugaban kwadagon, Boniface Stephen ne ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce har yanzu ‘yan bindigar ba su tuntube su ba tukunna.
Kakakin Rundunar ’yan sanda na jihar, ASP Leha Reform ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai ya ce har yanzu babu wanda ya tuntubi iyalan mutumin, kuma tuni jami’ansu suka dukufa wajen ceto shi.
Mun sami labarin sace shugaban Kungiyar Kwadago na Jihar Taraba a gidansa dake Sunkani da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka yi, amma muna nan muna kokarin kubutar da shi,” inji kakakin.