✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Janar Tsiga ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga

Maharan sun ci gaba da riƙe Janar Tsiga bayan karɓar kuɗin fansa daga hannun iyalansa.

Birgediya-Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga.

An sace Janar Tsiga, wanda Tsohon Shugaban Hukumar NYSC ne, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025.

Hakazalika, aharan sun sace mutum tara a tare da shi a lokacin da suka kai harin.

Duk da cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa, ’yan bindigar sun ci gaba da tsare shi na tsawon makonni.

Rahotanni sun nuna cewa har yanzu ba a san adadin kuɗin da aka biya a matsayin kuɗin fansar ba.

Wasu sun ce Naira miliyan 60 aka biya, amma wasu majiyoyi masu tushe sun ce an biya sama da haka.

Wani daga cikin iyalansa ya bayyana cewa bayan maharan sun karɓi kuɗin, sai suka yi shiru har na tsawon mako guda, kafin daga bisani su kira iyalansa a ranar 11 ga watan Maris, inda suka ba shi ya yi magana da su.

Daga baya, sun sake neman ƙarin kuɗi, amma iyalan nasa ba su ƙara musu ba.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa yanzu haka yana Jihar Zamfara, wanda daga nan za a kai shi Abuja.

Wani jami’in soja ya tabbatar da sakinsa, inda ya ce yana cikin ƙoshin lafiya.