An ceto yara takwas da aka yi safarar su daga Jihar Taraba ta hanyar haɗin gwiwar ma’aikatar mata da ci gaban ƙananan yara ta Jihar Taraba da Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP).
Kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban yara ta jihar Taraba, Misis Mary Sinjen ta ce yaran da aka ceto sun fito ne daga ƙauyen Minda da ke Ƙaramar hukumar Lau a Jihar Taraba.
- Adadin waɗanda suka mutu a harin Filato ya kai 52
- Boko Haram: An kashe ɗan sanda a sabon hari a Borno
A yayin da take zantawa da manema labarai a Jalingo, ranar Juma’a ta ce an yaudari yaran daga unguwar su aka yi safararsu zuwa jihohin Kudu maso Gabas.
Ta ce, sun gano su kuma sun ceto su a garin Aba, a Onitsha da kuma wani ɓangare na Jihar Imo tare da iƙirarin waɗanda suka yi safarar su da cewa su marayu ne.
Ta bayyana cewa, an damƙe masu aikata safarar ne a garin Gembu da ke ƙaramar hukumar Sardauna, a lokacin da suke gudanar da haramtattun aikinsu, wanda ya kai ga ceto yaran takwas, yayin da wasu da dama da aka yi safarar su ba a kai ga ceto su ba.
Waɗanda aka yi safarar ta su a ƙarshe sun sake haɗuwa da iyayensu a watan Maris 2025, sun tabbatar da cewa an sayar da su ba tare da sanin iyayen su ba.
“Bayan ɗaukar matakin gaggawa da ma’aikatar ta yi da kuma Hukumar NAPTIP, an dawo da takwas daga cikin yaran Jihar Taraba cikin lafiya.