✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe ’yan bindiga da ƙwato shanun sata 1000 a Taraba 

'Yan bindigar sun shigo Jihar Taraba ne daga Jihar Filato domin aikata ta’addanci tare da sace shanu.

Sojojin da suke aiki a ƙarƙashin rundunar birget ta 6 da ke garin Jalingo a Jihar Taraba sun kashe ’yan bindiga biyu tare da ƙwato shanu guda dubu ɗaya daga hannun ɓarayin shanu.

Muƙaddashin Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojoji ta birget ta 6 da ke garin Jalingo, Kyaftin Oni Olubodunde ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a garin Jalingo a ranar Juma’a.

Ya ce, nasarar ƙwato shanu tare da kashe ’yan bindigar ya kasance ne biyo bayan wani bayanan sirri da rundunar ta samu dangane da shuguban wasu guggun ’yan bindigar akan bubura talatin inda suka shiga wani yanki na Ƙaramar hukumar Karim Lamiɗo domin satar shanun makiyaya.

Kyaftin Oni ya bayyana cewa, yan ta’addan sun shigo Jihar Taraba ne daga Jihar Filato domin aikata ta’addanci tare da sace shanu.

Ya ƙara da cewa, ’yan ta’addan sun shiga yankin Jebjeb ne domin satar shanu a wasu rugagen Fulani, amma dubunsu ta cika inda sojojin suka kashe biyu daga cikinsu kuma suka fatattaki sauran tare ƙwato shanu har dubu ɗaya waɗanda su ’yan ta’addan suka sace.

Ya ce, a halin yanzu sojojin na tantace masu shanu domin a mayar masu da shanun su.