Iyayen Abdulsalam Rabi’u Faskari, wanda aka sace tare da mahaifinsa a Jihar Katsina, sun bayyana cewa sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga ba tare da biyan kuɗin fansa ba.
Abdulsalam, wanda ya lashe gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa da aka gudanar a Jihar Kebbi, an sace shi tare da mahaifinsa da wasu makonni biyu da suka gabata, bayan Gwamnan Katsina ya karrama shi.
- Talakawa su girmama shugabanni yayin bayyana matsalolinsu — Sarkin Musulmi.
- Babu tsamin dangantaka tsakaninmu da Gwamnan Sakkwato — Sarkin Musulmi
Mahaifinsa, Malam Rabiu Zakariya Faskari, ya shaida cewa suna tsare a hannun ’yan bindiga a Katsina har sai da wani babban ɗan bindiga mai suna Yellow daga Zamfara ya zo ya karɓe su da ƙarfi.
“Ya yi wa masu garkuwa duka kafin ya tafi da mu,” in ji shi.
Ya ce an yi ciniki kan fansa amma Yellow ya ƙi yarda.
“Muna ta addu’a har ranar Juma’a da aka zo aka ce mu fito mu tafi. Yaransa suka ɗauke mu suka kai mu wani gari, daga nan muka yi tafiyar awa huɗu kafin muka samu mota.”
Malam Rabiu, ya ce da suka hau babur sai direban ya shaida musu cewa an kashe Yellow.
“Ashe mutuwarsa ce ta sa yaransa suka sake mu muka koma gida.”