Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba.
Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka yi ta taimakon kai don taimakawa matafiya a kan hanya.
- Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya kama da wuta a Legas
- Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato
Gadar taimakon kai da aka gina a madadin babbar gadar da ta rufta watanni bakwai da suka gabata, ta kasance hanyar shiga ga masu ababen hawa da ke bin hanyar.
Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas ne ya bayar da kwangilar sake gina gadar a watan da ya gabata amma har yanzu ba a kai ga kwangilar zuwa wurin ba.
Masu ababen hawa da ke bin hanyar Jalingo da Wukari, an tilasta musu karkata zuwa hanyar garin Garba-Chede da ke ƙaramar hukumar Bali domin ci gaba da tafiya.
Masu ababen hawa da suka maƙale a ranar Laraba sun bayyana rashin jin daɗinsu kan gazawar gwamnatin tarayya na sake gina gadar kafin damina ta fara.
Wani direban babbar mota mai suna Bello Adamu ya ce direbobi da masu ababen hawa ba su ji daɗin yadda ba a sake gina gadar cikin lokaci mai kyau ba, kuma yanzu damina ta fara kawar da gadar wucin gadi a madadin babbar gadar.