’Yan bindiga sun bude wa wata motar bas mai cin mutum 18 wuta a kauyen Ochonyi-Omoko da ke kan hanyar Abuja zuwa Lokoja a jihar Kogi, sannan suka sace fasinjojin cikinta.
Daya daga cikin fasinjojin da ya kubuta daga motar mai suna Benjamin Isaac, ya ce lamarin ya faru ne wajen misalin karfe 8:03 na daren Laraba.
- Raliya Ta Dadinkowa Za Ta Shige Daga Ciki
- Gwamnati na duba yiwuwar haramta acaba a Najeriya baki daya
Ya ce maharan, wadanda suka buya a cikin daji, sun bude wa motar tasu wuta ne, lamarin da ya sa tayoyinta suka sace.
“Sun bude wa tayoyin baya na motar wuta, inda ala tilas direbanmu ya tsaya. Bayan motar ta kwace ta sauka daga kan hanya, sai maharan suka fito daga daji suka tisa keyarmu zuwa cikin dajin,” inji Benjamin.
Ya ce ya sami nasarar guduwa tare da wasu fasinjoji da suka gudu cikin daji.
Benjamin ya kuma ce tun da farko ya hau motar ce a gefen hanya a Zuba da ke Abuja, a kan hanyarsa ta zuwa Okpella a jihar Edo.
Wani jami’in sintiri a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yana yin alwalar Sallar Isha ne lokacin da ya ji karar harbe-harbe.
“Ina idar da sallar sai na debi jami’aina muka rankaya wajen, inda muka ga motar bas din a gefen hanya babu fasinjoji a ciki,” inji shi.
Ya ce daga bisani ya gano cewa fasinjojin da ke cikin motar an yi awon gaba da su.
Amma ya ce dakarunsa na ci gaba da farautar mutanen a cikin daji da nufin ceto su.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda Jihar ta Kogi, SP Williams Ovye Ayah, bai daga kiran wakilinmu ba ko amsa rubutaccen sakon da ya aike masa har zuwa lokacin hada wannan rahoton.