✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi amai sun lashe kan Daliban Afaka

’Yan bindigar da kansu suka koma neman iyayen daliban suna bukatar kudin fansa

’Yan bindigar da suka sace daliban Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Jihar Kaduna sun yi amai sun lashe kan maganar da suka yi cewa ba za su tattauna da kowa ba sai gwamnati.

Aminiya ta gano yadda ’yan bindigar da kansu suka koma neman daidaikun iyayen daliban suna bukatar kudin fansa, bayan Gwamna Nasir El-Rufai ya ce sam gwamnatinsa ba za ta tattauna da su ba ko ta ba su kudin fansa, kuma zai hukunta duk wanda ya yi hakan.

A lokacin da suka yi garkuwa da daliban, ’yan bindigar sun kira iyayen suka yi musu kashedi cewa kada su kuskura su neme su, su da gwamnati kadai za su yi magana.

Daga baya sun sako 10 daga cikin daliban —maza bakwai mata uku— bayan tattaunawa da masu shiga tsakani da ake kyautata zaton zai kai ga sako daukacin daliban su 39.

Wasu daga cikin iyayen daliban da masu garkuwa suka tuntuba sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar na barazanar cutar da su idan ba su biya kudaden fansan ba.

“Sun sa ’yata ta kira ni, tana kuka tana roko a nemo kudin fansar, idan ba haka ba kuma za su kashe ta,” inji daya daga ciki iyayen.

Wata daga cikinsu ta ce ’yan bindigar sun yi barazanar cewa ba za ta taba ganin ’yarta ba, matukar ita da sauran iyayen ba su kawo kudin fansa Naira miliyan 500 da suka bukata ba.