✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun tsere da bindigar soja bayan kashe shi

'Yan bindigar sun kashe sojan yayin da yake bakin aikinsa a yakin Apoi.

Wasu mutane da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kashe wani soja da ke rangadin bututun iskar gas a yankin Apoi na Karamar Hukumar Ijaw ta Kudu a Jihar Anambra, sannan suka tsere da bindigarsa.

Wannan hari na zuwa ne, kwanaki kadan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da jami’in tsaron cikin gida na NSCDC tare da yin awon gaba da wasu makamai na sa, a Karamar Hukumar Ekeremor dake jihar.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa Aminiya cewar, mutane na cikin fargabar ka da ‘yan bindigar suka kawo wani harin.

Tuni wasu mazauna yankin suka yi kaura zuwa wasu kauyuka dake makwabtaka da su, saboda gudun abin da ka iya zuwa ya dawo.

Rahotanni sun bayyana cewa sojan na bakin aiki ne a Apoi yayin da ‘yan bindigar suka kashe shi a Yammacin ranar Litinin.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar Operation Delta Safe (OPDS), Victor Olukoya, ya ce Kakakin Hukumar Tsaron Kasa ne ke da ikon yin magana kan lamarin.

Shugaban yankin na Apoi da aka kashe sojan, Mista Jepthah Keme, ya yi Allah wadai da lamarin, sannan ya yi alkawarin za su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan da suka dace domin gano wanda suka aikata laifin.

Haka kuma, ya ce wannan yanki nasu ya yi shahara a matsayin wata cibiya ta wanzar da zaman lafiya.

“Yankinmu waje ne da ake wanzar da zaman lafiya, kuma za mu ci gaba da ba wa jami’an tsaro bayanan da suka dace don gano wanda suke da hannu a kisan.

“Wanda suka aikata hakan ba daga Apoi suke ba, don yankinmu ba a tashin hankali. A sanadin haka gashi nan mutane da yawa sun kauracewa yankin,” in ji Mista Keme.