Mutane sun yi kaura daga wasu kauyuka biyar bayan ’yan bindiga sun fatattake su tare da sace musu shanu akalla 100 a Karamar Hukumar Kebbe ta Jihar Sakkwato.
Kauyukan da ’yan bindigar suka tayar a karamar hukumar su ne Ugunsi da Asarara da Sangi da Mai Kurfana da Gwandi.
- Mutum 7 sun rasu bayan rushewar gini a Jigawa
- Dalilin da muka zabi sulhu da ’yan bindiga — Shugaban Yankin Isa
Wata majiyar ta ce ’yan bindigar sun kori al’ummomi da yawa a karamar hukumar.
Ta ce tana kyautata zaton ’yan bindigar sun fito ne daga jihohin Zamfara da Kebbi da Neja da ke makwabtaka da Sakkwato inda ake ci gaba da gudanar da ayyukan soji, kuma a yanzu ’yan bindigar sun samu mafaka Kebbe saboda ciyayi dake yankin.
Majiyar ta ce hare-haren ’yan bindiga da ke kai hare-hare a kauyuka tare da sace wa jama’a dabbobi da amfaninin sun zama ruwan dare a kowace shekara a karamar hukumar.
Ta kuma roki Gwamnatin Tarayya da ta kawo dauki a yankin ta hanyar gudanar da aikin soja kamar yadda aka yi shekaru uku da suka wuce.
Wata majiyar ta ce a a ranar Talata ma, “’Yan bindiga sun koma Gwandi inda suka hana mutane cire amfanin gonarsu, bayan sace masu shanu da suka yi.”
Da aka tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, DSP Sanusi Abubakar, ya ce ba shi da masaniya kan harin da aka kai Gwandi, amma zai tuntubi wakilinmu daga baya.