✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sako daliban makarantar Bethel 28 a Kaduna

Sai dai har yanzu akwai ragowar dalibai 80 a hannun 'yan bindigar.

’Yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban makarantar Bethel Baptist Academy da ke kan hanyar Kaduna zuwa Kachia a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna sun sako 28 daga cikinsu ranar Lahadi.

Biyu daga cikin daliban dai a baya sun sami nasarar guduwa daga hannun masu garkuwar, yayin da ’yan bindigar da kansu suka saki daya saboda dalilan rashin lafiya.

A ranar 5 ga watan Yuli ne dai ’yan bindigar suka kai hari makarantar tare da sace dalibai da dama da cikinta.

Sun dai bukaci a basu Naira dubu 500 a kan kwanne dalibi a matsayin kudin fansarsa.

Kimanin dalibai 121 ne aka sace a wancan lokacin.

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Kaduna, Rabaran John Hayab ya ce har yanzu akwai kimanin dalibai 80 a hannun masu garkuwar.

Ya kuma ce daliban da suka kubuta za su sadu da iyalansu nan ba da jimawa ba.

%d bloggers like this: