’Yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban makarantar Bethel Baptist Academy da ke kan hanyar Kaduna zuwa Kachia a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna sun sako 28 daga cikinsu ranar Lahadi.
Biyu daga cikin daliban dai a baya sun sami nasarar guduwa daga hannun masu garkuwar, yayin da ’yan bindigar da kansu suka saki daya saboda dalilan rashin lafiya.
- Mutum 145 ne za su jagoranci shirya auren Yusuf Buhari da ’yar Sarkin Bichi
- A karo na 6, an sake tsawaita wa’adin hada layukan waya da lambar NIN
A ranar 5 ga watan Yuli ne dai ’yan bindigar suka kai hari makarantar tare da sace dalibai da dama da cikinta.
Sun dai bukaci a basu Naira dubu 500 a kan kwanne dalibi a matsayin kudin fansarsa.
Kimanin dalibai 121 ne aka sace a wancan lokacin.
Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar Kaduna, Rabaran John Hayab ya ce har yanzu akwai kimanin dalibai 80 a hannun masu garkuwar.
Ya kuma ce daliban da suka kubuta za su sadu da iyalansu nan ba da jimawa ba.