Shugaban Kasa Bola Tinubu ya kaddamar da aikin sake gyaran babban titin Abuja-Kaduna-Zariya-Kano, wadda ke da matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Arewacin Najeriya.
Da yake jawabi a taron kaddamarwar a Kagarko, Jihar Kaduna, Gwamna Uba Sani, ya bayyana yadda aka yi watsi da hanyar da kuma irin mummunan tasirin da hakan ya yi ga rayuka da ci-gaban tattalin arziki.
Gwamna Uba Sani, ya yaba wa Tinubu bisa farfado da aikin, yana mai nuni da muhimmancin hanyar a matsayinta na mafi yawan zirga-zirgar ababen hawa a Arewa.
Da yake ba da tabbacin kamma aikin a cikin watanni 14, Tinubu wanda Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce za a gina titin ne da kankare, kamar babbar hanyar Legas zuwa Kalaba.
- An kama kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
- An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo
- Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken Tinubu
Ministan ya kara da cewa aikin zan dangana har zuwa filin jirgin sama na Kano, kuma za a sanya kyamarorin CCTV gaba daya a tsawon titin, wanda sabon dan kwangila ne zai aiwatar.
Ya ce, shugaban kasa ya amince da naira biliyan 252 don muhimman sassan aikin, inda aka riga aka biya kashi 30%, yanan mai yaba muhimmiyar rawar da Gwamna Uba Sani ya taka a aikin.