✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kama ’yan bindiga 12 a Nijar

Dakarun tsaron ƙasar sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu a yankin Falmey.

Rahotanni daga Nijar na cewa dakarun tsaron ƙasar sun yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu tare da kama ‘yan bindiga 12 a yankunan Dosso da Diffa na ƙasar.

Kafar watsa labarai ta ActuNiger ta ruwaito cewa a Boumba da ke yankin Dosso ne dakarun tsaron ƙasar suka yi nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu bayan dakarun da ke sintiri sun yi arangama da ‘yan ta’addan da suka je daga yankin Falmey.

Kazalika ranar Alhamis ne dakarun tsaron ƙasar suka yi nasarar kama ‘yan bindiga 12 a ƙauyen Jagada da ke yankin Diffa.

TRT ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan bindiga suka kai farmaki a ƙauyen kuma suka fara yi wa mutane ƙwace.

Ana cikin haka ne mutane suka kira dakarun tsaron da ke ƙauyen Kablewa mai maƙwabtaka kuma dakarun suka kai wa mutanen ƙauyen Jagada ɗauki, inda suka yi nasarar kama 12 daga cikin maharan tare da ƙwace bindigogi biyu ƙirar AK47.

Domin ƙarfafa tsaro a ƙauyen da kuma hana ramuwar gayya daga ‘yan bindigar, an samar da ‘yan sintiri na dindindin da suke sun yawo a cikin ƙauyen.

An garzaya da mutane biyun da suka ji rauni a harin asibitin Kablewa inda a yanzu suke samun kulawa.

Har wa yau, dakarun Nijar sun yi nasarar kama mutum biyu masu yi wa ISWAP safarar kayayyaki a yankin Diffa.

Waɗannan nasarorin na zuwa a lokacin da sojin ƙasar ke ƙoƙarin katse hare-haren ‘yan ta’adda da ƙasar ke fama da su.