✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sako Daliban Afaka

A halin yanzu daliban na hanyarsu da zuwa garin Kaduna bayan ’yan bindigar sun sako su.

’Yan bindiga sun sako ragowar daliban Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da suka yi garkuwa da su a Jihar Kaduna.

Wani daga cikin wadanda suka karbi daliban ya shaida wa Aminiya a yammacin Laraba cewa fitaccen malamin Islama, Shaik Ahmad Abubakar Gumi ne ya sa baki aka sako su.

Ya ce a halin yanzu daliban na kan hanyarsu ta zuwa garin Kaduna kuma an kubutar da su ne bayan Shaik Gumi ya tattauna masu garkuwar da taimakon tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo.

Majiyarmu ta tsaro ta ce za a fara kai daliban Hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, inda za a duba lafiyarsu kafin a sada su da iyalansu.

“Tun jiya da dare muke nan tare da jami’an lafiya muna jiran isowarsu amma ba su zo ba. Daga baya masu shiga tsakani suka kira da safe cewa mu kasance cikin shiri kuma tun da safen muke jiran su,” inji shi yana mai cewa duk ragowar daliban su 29 ne aka sako.

Daliban na daga cikin 39 da ’yan bindigar suka kutsa cikin kwalejin da ke Afaka suka yi awon gaba da su wata biyu da suka gabata.

Bayan iyaye da hukumar makarantar sun biya kudin fansa, an sako 10 daga cikinsu.

Ko a ranar Talata, iyayen daliban da takwarorinsu dalibai sun gudanar da zanga-zangar lumana a Majalisar Tarayya, tare da neman a kawo musu dauki wajen kubutar da daliba.

Da farko masu garkuwar sun bukaci Gwamnatin Jihar ta biya su kudin fansa Naira miliyan 500, amma Gwamna Nasir El-Rufai ya ce allamabaran, ko tattaunawa da su ba zai yi ba, ballantana biyan su ko sisi.

Daga baya sai suka koma tuntubar iyayen daliban suna neman su biya kudi domin a sako musu ’ya’yansu.

Sace daliban manyan makarantu

Tun bayan harin na Kwalejin Afaka, ’yan bindiga sun yi yukurin sace dalibai a wata makarantar sakandaren kwana ta samari zalla a Karamar Hukuamr Ikara, amma jami’an tsaro suka fatattake su.

A kokarin ceto daliban Kwalejin, Shugaba Buhari ya ba da umarnin harbe duk wanda aka gani da bindiga kirar AK 47 ba bisa ka’ida ba, umarnin da ake ganin ya yi tarnaki ga masu neman shiga tsakani, irinsu Dokta Gumi wurin tattaunwa da ’yan bindiga.

A watan Afrilu, ’yan bindiga sun kutsa Jami’ar Greenfield da ke Kasarami a Jihar ta Kaduna, suka yi garkuwa da dalibai.

Masu garkuwar da da farko suke neman a ba su kudin fansa Naira miliyan 800 sun kashe biyar daga cikin daliban domin tursasawa don a biya su.

Daga baya sun rage kudin fansar zuwa Naira miliyan 100 da babura 10 tare da barazanar yi wa daliban kisan dauki dai-dai idan ba a biya bukatunsu zuwa ranar Talata ba.

A ranar Talata, Aminiya ta kawo rahoto cewa an sako daya daga cikin daliban, amma babu bayani game da kudin fansa.