’Yan bindiga sun sako basaraken nan na Jihar Neja, Dodo na Wawa, Dokta Mahmud Ahmed Aliyu.
Babu dai cikakkun bayanai har yanzu a kan sako basaraken, amma Aminiya ta gano cewa masu garkuwar da shi na kan tattaunawa da gwamnatin Jihar.
- An kama mutum 5 kan zargin datse kan karuwa don yin tsafi
- Mahara sun kashe shanu 10, sun raunata 23 a Filato
Sai dai duk kiran wayar da wakilin Aminiya ya yi a fadar don tabbatar da ko an biya kudin fansa ba a amsa ba.
Amma wani mazaunin yankin ya ce ya ga basaraken ne kawai ya shiga fadarsa da yammacin Juma’a
“Ba mu zauna da shi ba don jin me ya faru. Amma zan iya tabbatar da cewa ya dawo yau [Juma’a] da yamma,” inji majiyar.