✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ceto ɗalibai 10 sun kashe ɗan bindiga a Edo

An kashe ɗaya daga cikin ’yan garkuwan a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan…

Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Edo sun ceto ɗalibai 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Edo.

An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigan, a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi.

Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ɗaliban ne a ranar 16 ga Afrilu, 2025, a kan hanyarsu ta zuwa Jami’ar Babcock don taron shekara-shekara na GYC Africa.

Kakakin rundunar, SP Kontongs Bello, wanda ya tabbatar da ceton, ya ce da samu rahoton sace daliban, kwamishinan ’yan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya tura ’yan sanda na musamman tare da ’yan banga da maharba cikin daji domin ceto su da kuma kama waɗanda ake zargi.

Ya ce a lokacin aikin, an kashe ɗaya daga cikin ’yan garkuwan, yayin da sauran suka tsere da raunukan harsashi.
“Jami’an sun yi taka-tsan-tsan don guje wa asarar rayukan fararen hula saboda ’yan garkuwan sun yi amfani da waɗanda aka sace a matsayin garkuwa.”

A cewarsa, wani Sufeton ɗan sanda ya samu raunin harbin bindiga a lokacin aikin, kuma yana samun kulawa a asibiti a halin yanzu.

Ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin cafke ‘yan garkuwan da suka tsere.