✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun saki bidiyon hakimin da suka sace a Sakkwato

Hakimin ya roƙi gwamnatin jihar da ta kai masa ɗauki.

Hakimin gundumar Gatawa a ƙaramar hukumar Sabon Birni, Isa Muhammad Bawa, ya roƙi gwamnatin Jihar Sakkwato da ta taimaka masa, saboda wa’adin da ’yan bindiga suka bayar na biyan kuɗin fansarsa.

A cikin wani faifan bidiyo da ya karaɗe Intanet, an ga hakimin mai shekara 74, wanda ya shafe kwanaki 22 a hannun mahara, yana sanye da farar riga da jini a jikinta, hannayensa a ɗaure.

Ko da yake jaridar Aminiya ba ta tabbatar da sahihancin bidiyon ba.

Aminu Boza, wanda ke wakiltar Sabon Birni a Majalisar Dokokin Jihar, ya tabbatar cewa hakimin ne a cikin faifan bidiyon.

A cikin bidiyon, hakimin ya ce, “Ina sanar da iyalina, abokaina, da shugabanni cewa yau (Laraba) ita ce rana ta ƙarshe. Idan suna so su taimake ni, su yi hakan yanzu.”

Ya ƙara da cewa, “Na rantse da Allah Maɗaukakin Sarki cewa ’yan bindigar nan sun gaji saboda sun yi ƙoƙarinsu, amma babu wani abu da gwamnati ta yi. Na daɗe ina yi wa gwamnati hidima a masarauta kusan shekara 45, kuma ina fata za su taimake ni.”

An sace basaraken tare da ɗansa da ƙaninsa a Kwanan Maharba kan hanyar Goronyo-Sabon Birni yayin da suke dawowa daga Sakkwato.

Maharan da farko sun nemi kuɗin fansa na Naira biliyan ɗaya, amma daga bisani suka rage zuwa Naira miliyan 500.