’Yan bindiga sun sake kai hari karo na uku a kauyaku biyu na Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna inda suka sake kashe mutum 23 tare da raunata wasu da dama.
Wani mazunin yakin da Aminiya, ta tattauna da shi kuma ya nemi a sakaya sunansa, lamarin ya auku ne ranar Litinin da da daddare zuwa wayewar garin Talata.
- Tinubu ya soke bikin ranar haihuwarsa saboda harin Kaduna
- Buhari ba shi da tausayi, ya yi murabus kawai —Tsohon hadimin Ganduje
Ganau din ya ce tun da misalin karfe 5:00 na yamma ne aka fara ganin maharan a kan babura sun dawo dauke da bindigu, inda suka sanar da jami’an Tsaro.
Kauyakun da ’yan bindiga suka kutsa su ne Anguwar Maiwa da Kanwa duk a cikin Karamar Hukumar.
Ganau din ya ce a sakamakon harin, ’yan bindigar sun sake kashe musu mutum 23, amma ya zuwa yanzu sun gano gawar mutum 22 saura gawar mutum daya.
Ya kuma ce maharan sun kuma raunata mutane da dama, sun kuma kona musu gidaje da Masallatai da Coci-Coci, duk a daren.
Sai dai ya ce a wannan karon, jami’an tsaro na hadin gwiwa sun kawo dauki kuma sun ceto wasu daga cikin mutanen da aka sace, su kuma maharan an kashe wasu daga cikin su da dama.
Sai dai duk kokarin kiran wayar kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige da wakilinmu ya yi, don jin ta bakin rundunar, ya ci tura.