Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wata tsohuwa mai shekara 90 a garin Kurya Madaro dake Karamar Hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara.
Wata majiya a kauyen ta ce, bayan tsohuwar da aka dauke, sun kuma tafi da wasu matasa hudu wanda biyu daga cikinsu yan gida daya ne.
- An kama uwa da ‘ya’yanta a kan fashi da makami a Kano
- Masu garkuwa da ‘yan sanda a Katsina na neman kudin fansar N100m
Rahotanni sun ce ’yan bindigar sun afkawa garin ne da misalin karfe 12 na daren asabar inda suka yi awon gaba da tsohuwar mai suna Hajiya Aisha bayan da suka gaza kama danta, Alhaji Danbaba, wanda dan kasuwa ne.
“Dan ta suka zo nema, da basu same shi ba dai suka dauki mahaifiyarsa da ba ta iya ko tafiya saboda tsufa,” inji majiyar.
Kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar, SP Muhammad Shehu ya ci tura, saboda rashin samunsa a waya har zuwa lokacin hada wannan rahoto.