’Yan bindiga sun yi garkuwa da Shugaban Babban Asibitin Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru a Jihar Zamfara.
An yi garkuwa da Dakta Mansur Muhammad a wani sanannen wuri mai hadarin gaske da ake kira Mashayar Zaki a kan hanyar Gusau zuwa Dansadau.
- A soma laluben watan Dhul-Hijjah daga ranar Laraba —Sarkin Musulmi
- Yadda aka damfari masu neman gidan haya Naira miliyan 60 a Legas
Shugaban Kungiyar Likitocin Najeriya reshen Jihar Zamfara, Dakta Mannir Bature ne ya bayyana hakan yayin ganawarsa da wakilinmmu a ranar Talata.
A cewarsa, Kungiyar Likitocin ta yi matukar kaduwa da rahoton sace abokin aikinsu, Dakta Mansur Muhammad.
“Muna kira ga mambobinmu da sauran jama’a da su sanya shi da sauran wadanda aka kama a cikin addu’o’insu, yayin da kungiyar ke aiki da hukumomin da abin ya shafa don ganin an sako shi cikin aminci,” in ji Dokta Bature.
Hanyar Gusau zuwa Dansadau abar firgici ce ga matafiya da dama, inda an yi garkuwa da daruruwan mutane a kan hanyar yayin da kuma da dama sun rasa rayukansu.
Aminiya ta samu cewa, a yanzu galibi fasinjoji sun dauke wa hanyar kafa, inda sai an samu jami’an tsaro sun yi rakiyar matafiya zuwa garin Dansadau ko Gusau saboda babu wanda zai kuskura ya bi hanyar ba tare da rakiyar jami’an tsaron ba.
“’Yan bindiga suna tare motoci su yi awon gaba da mutane, a wani lokacin kuma sai kawai su bude wuta kan motocin da ke tafiya.
“An samu asarar rayuka da dama a dalilin haka,” a cewar wani mazaunin garin mai suna Bala Ali Isah.