✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace shanu 300 a Zamfara

’Yan bindigar sun shafe awa biyu suna cin karensu babu babbaka a Dansadau.

’Yan bindiga sun kai hari a Zamfara inda suka yi awon gaba da shanu da dama tare da fasa shagunan mutane a garin Dansadau na Karamar Hukumar Maru ta Jihar.

Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewar ’yan bindigar da adadinsu ya kai 150 sun yi wa garin kawanya da misalin karfe 4 na yamma, suka kora shanu 300 zuwa daji.

“Sun fasa shagunan mutane suka kwashi kaya da yawa, saboda rashin jami’an tsaro a kusa, sai da suka shafe awa biyu suna mana barna.

“A lokacin kowa ya gudu domin tsira da rayuwarsa, ko’ina ya yi tsit ba bukowa, daga nan ne suka yi awon gaba da shanun,” kamar yadda Bilyaminu Dansadau ya shaida wa Aminiya.

Ya kara da cewa ’yan bindigar sun dauki lokaci suna harbi a iska yayin da suke kora shanun zuwa daji.

’Yan bindigar sun kai farmakin ne bayan kashe wani dan bindiga da wasu ’yan bindiga suka yi a garin a kwanakin baya.

Zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto, wakilinmu ya kasa samun kakakin ’yan sandan Jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu don samun karin bayani game da harin na Dansadau.