Akalla mutum 44 ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da su a kauyen Kanwa da ke Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara.
Mazauna yankin sun ce maharan sun yi wa kauyen kawanya ne cikin dare, inda suka rika bi gida-gida suna kwasar mutane, galibi mata da kananan yara.
A baya-bayan nan dai, an dan sami sa’idar yawan satar mutane a kauyukan jihar ta Zamfara, amma bisa ga dukkan alamu a ’yan kwanakin nan, cikin mazauna kauyukan ya fara durar ruwa saboda yadda lamarin ya sake dawowa.
Ana dai zargin cewa rikakken dan bindigar nan na yankin, Dankarami ne ya shirya satar mutanen.
Aminiya ta rawaito cewa Dankarami dai ya jima yana addabar mazauna yankunan Zurmi zuwa Birnin Magaji zuwa Jibiya a kan iyakar jihohin Zamfara da Katsina.
A cewar wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, har zuwa lokacin hada wannan rahoton barayin ba su tuntubi iyalan mutanen ba domin neman kudin fansa.
A wani labarin kuma, mazauna garin Moriki sun fara yin karo-karo domin tara Naira miliyan 20 a matsayin ‘Kudin Kariya’ da ’yan bindiga suka bukata daga wajensu.
A cewar mazauna yankin, ana bi gida-gida ne domin tattara kudin da za a kai wa ’yan ta’addan da ke karkashin Bello Turji.
Dan ta’addan da tawagarsa dai sun yi alkawarin cewa za su kare yankin daga mahara matukar aka ba su kudin kamar yadda suka bukata.
Garin Moriki dai wanda ke kan hanyar Shinkafi zuwa Kauran Namoda ya sha fama da hare-hare a baya, ciki har da na sace wani malami a wata makarantar sakandaren ’yan mata da ke garin.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, wakilinmu bai samar damar jin ta bakin Kakakin Rundunar’Yan Sandan Jihar, Mohammed Shehu ba.