Rahotanni sun bayyana cewa wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutum 17 a Unguwar Maje da ke kauyen Jere na Karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru da sanyin safiyar ranar Litinin, inda maharan suka farmaki yankin a kan babura.
- NAJERIYA A YAU: ‘Illolin kaurace wa zabe sun fi na kada kuri’a yawa’
- Gwamnati ta ba da umarnin toshe duk layukan wayar da ba a hada da NIN ba
Harin na zuwa ne kasa da sa’a 24 bayan Sufeto Janar na ’Yan sanda, Usman Alkali Baba ya ziyarci babbar hanyar da ke tsakanin Kaduna da Abuja.
Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce mutanen yankin sun shiga dimuwa da fargaba lokacin da ’yan bindigar suka kai hari yankin.
“Mun shiga tashin hankali lokacin da ’yan bindigar suka yi garkuwa da mutum 22, amma biyar daga cikinsu sun yi nasarar tserewa lokacin da suke kokarin tafiya daji da su,” a cewarsa.
Ya kara da cewa, har yanzu ’yan bindigar ba su tuntubi ‘yan uwan wadanda suka sace don jin yadda makomarsu za ta kaya ba.
Sai dai hakar wakilinmu ba ta cimma ruwa ba a yayin da ya yi kokarin jin ta bakin shugaban Karamar Hukumar ta Kagarko, saboda wayarsa na kashe.
Kazalika, shi ma kakakin ‘yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige wayarsa na kashe.