✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace mutum 1, sun harbe wani a Sakkwato

Kakakin 'yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar harin.

’Yan bindiga sun kai hari tashar motar Tambuwal da ke Karamar Hukumar Tambuwal a Jihar Sakkwato, inda suka yi awon gaba da wani dan kasuwa.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar.

Tambuwal dai mahaifar tsohon gwamnan jihar ne, Sanata Aminu Waziri Tambuwal.

Aminiya ta gano cewa ‘yan bindigar sun dinga harbe-harbe, wanda hakan ya sa al’ummar yankin suka tsere.

Sun kuma raunata wani mutum daya wanda a halin yanzu yana asibiti a kwance yana samun kulawa.

Wata majiya a yankin, ta shaida wa Aminiya cewa, ‘yan bindigar sun shiga yankin ne da nufin sace mahaifin wani dan kasuwa amma ba su yi nasara ba.

“Sai suka tafi da ɗansa, Paul,” in ji majiyar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmed Rufa’i, ya tabbatar da faruwar harin.

“Kun san Tambuwal gari ne da ke tsakanin hanyar Jihar Sakkwato da Jihar Kebbi.

“Mun sanar da ‘yan sanda da ke makwabtaka da Jihar Kebbi, kuma ana ci gaba da bincike,” in ji shi.