Wasu ‘yan bindiga kimanin su 40 sun yi awon gaba da mutane 23 yayin wani hari na safiyar ranar Alhamis da suka kai kauyen Kawu da ke Karamar Hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja.
Kansilan yankin, Abdulmumini Zakari ya bayyana cewa tun a ranar Laraba ‘yan bindigar suka shigo kauyen ta dajin Kuyeri wanda ya yi iyaka da jihohin Kaduna da Neja.
- Kotun Koli: Yau za a san ainihin Gwamnan Kano tsakanin Abba da Gawuna
- NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Huce Gajiya Cikin Sauki
Ya bayyana cewa, “maharan sun raba kansu gida-gida, inda wasunsu suka shiga fadar hakimin gundumar, Alhaji Abdurrahman Danjuma Ali, kuma suka yi awon gaba da dansa Lukman da matarsa, wadda ya aura makonni biyu da suka gabata.
“Wasu kuma sun kai hari gidan Alhaji Alhassan Sidi Kawu, Marafan Kawu kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP na unguwar Kawu, inda suka yi awon gaba da shi tare da ’ya’yansa hudu.”
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun kuma shiga harabar fadar Sarkin Pawan Kawu, Gambo S Pawa, inda suka yi awon gaba da shi tare da matansa biyu da wasu ’ya’yansa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, S.P Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin cikin wani sako da ta aiko wa wakilinmu.
“Eh tabbas wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kauyen Kawu da ke makwabtaka da Karamar Hukumar Kagarko ta Jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da mutane.
“Maganar gaskiya ita ce kusan mamaye kauyen ’yan bindigar suka yi gaba daya, kuma bayan sun yi abin suka yi suka tsere Jihar Kaduna,” inji ta.