Wasu ’yan bindiga sun yi awon gaba da mutum hudu yayin da suka yi dirar mikiya a wasu rukunin gidaje kashi biyu na unguwar Dutsen Reme da ke Karamar Hukuma Bakorin Jihar Katsina.
Lamarin a cewar mazauna rukunin gidaje na Low cost, ya faru ne da misalin karfe 10 na daren rana Juma’a yayin da ake zabga ruwan sama kamar da bakin kwarya.
- Kwankwaso da ma ba abokin tafiyar Shekarau ba ne a siyasa
- Kashe iyayena da na yi ‘Jihadi’ ne —Malamin Islamiyya
A cewar wani mai suna Ahmed Ridwani, ’yan bindigar sun ribaci ruwan saman da ke sauka wajen aikata wannan aika-aika ba tare da fuskantar wata tirjiya ba.
“Mutanen kauyen da ke kusa da Maska sun sanar da mu ta wayar tarho cewa ’yan bindigar masu yawa sun nufi inda muke, kuma nan take mun sanar da ’yan sanda da jami’an soji amma kafin isarsu tuni ’yan bindigar sun yi awon gaba da mutane hudu,” in ji Ridwan.
Malam Lawal Hamisu Maska, wanda ba ya nan a lokacin da aka kai hari gidansu, ya ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da makwabcinsa da suka haya a gida daya, Bishir Shitu Sallau wanda ma’aikaci ne a Babbar Kotun Funtua tare da wani Safiyanu, dalibi a Kwalejin Ilimi da ke Abuja.
“Ba na nan lokacin da ’yan bindigar suka kai hari gidan, amma kafin su iya shiga tuni Bishir da Safiyanu sun boye matansu a makewayi.
“Yayin da ’yan bindigar suka balle kofar, sun nemi matan sun rasa, lamarin da ya sanya suka yi awon gaba mazajensu.
Hamisu Maska ya kara da cewa karshen zamansa ke nan a gidan da kuma unguwar domi kuwa zai tattara ina-sa-ina-sa ya kara gaba.
“Ni ma’aikacin lafiya ne kuma aiki ne ya kawo ni Funtua daga Maska, wannan rashi kwanciyar hankali ya sa ba ni da wani zabi da wuce na koma kauyenmu,” in ji shi.
Aminiya ta ruwaito cewa, a daya kashin na rukunin gidaje da ke unguwar Dutsen Reme, ’yan bindiga sun yi awon gaba da Lauratu Jibril da kuma ’yan kishiyarta yayin da mijinsu, Malam Jibril ya tsallake rijiya da baya.
Safara’u Sanusi, kanwar matar da lamarin ya rutsa da ita, ta ce ’yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 9.45 na dare.
“Lauratu da mijinta Jibril ba su dade da aure ba don ko kwana talatin ba ta yi ba tarewa ba aka sace ta. Lokacin da ’yan bindigar suka kawo harin sai maigidanta ya haaura ta katanga ya tsere.
A cewar mazauna, kwanaki bakwai da suka gabata sai da ’yan bindiga suka sace mutum biyu a yankin.
A makon jiya ne ’yan bindigar suka sace wani Tajuddeen mai sana’ar faci da matar wani Tanimu Muhammad a Unguwar Maitandama.
Harin ’yan bindiga na makon jiya
A wani labarin mai nasaba da wannan, ’yan bindiga kimanin 20 sun kai hari kauyen Kabomo da ke Karamar Hukumar Bakori inda suka sace mutum 6 ciki har da wasu mata biyu masu juna biyu.
Salima Lawal, wata abokiyar zaman daya daga cikin matan da aka sace, ta ce ’yan bindigar suna kai hari ne da misalin karfe 12.15 na daren ranar Alhamis, inda suka sace mutum 6 a gidaje uku daban-daban.
Sai dai har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah wanda wakilinmu ya tuntuba bai kai ga tabbatar da faruwar lamuran ba.