✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun sace matashiya a Ondo, sun bukaci miliyan 10

Maharan sun bukaci a biya su miliyan 10 a matsayin kudin fansa.

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wata matashiya mai shekara 19, mai suna Adetutu Okinbaloye a unguwar Imoru da ke Karamar Hukumar Ose a Jihar Ondo.

Aminiya ta samu labarin cewa ’yan bindigar su bakwai dauke da makamai sun kutsa cikin wani gida inda suka tafi da ita bayan sun raunata ’yar uwar mahaifiyarta da wuka.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, Fumilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a ranar Talata a Akure.

Sai dai wata majiya a unguwar ta ce maharan sun tuntubi iyalan matashiyar inda suka bukaci a biya su Naira kudin fansa Naira miliyan 10.

A wani labarin makamancin kuwa, an gano gawar wani mutumi da aka ce direban motar haya ne dan garin Idanre a Akure.

Wani ganau ya ce an jefar da gawarsa ne a kusa da babbar tashar mota ta Benin a Akure.

An kuma tattaro cewa wasu da ake zargin masu tsafi ne suka kashe shi yayin da suka yanke wasu sassan jikinsa.