’Yan fashin daji sun kai hari tare da sace mata hudu a Babban Asibitin Kurfi da kr Jihar Katsina.
Da misalin karfe 10.45 na daren Laraba ne suka kai harin, suka harbi mai gadin sannan suka yi garkuwa da matan.
Cikin matan da suka sace har da matar wani ma’aikacin lafiya da ke bakin aiki, wanda ya tsallake rijiya da baya.
Wata majiya mai tushe a garin Kurfi ta shida mana cewa da farko ’yan bindigar sun je asibitin ne ba tare da makami ba.
Bayan mai gadin ya tare su yana musu tambayoyi, sai aka samu sa-in-sa a tsakaninsu, “ssi ya yi sauri ya kulle babbar ƙofar shiga asibitin suna daga waje, bai sani ba, ashe sauransu da ke ɗauke da makamai suna gefe.
“Sai suka haura katanga suka shigo suka harbe shi a ciki; an ɗauka ma ya mutu, amma aka ba shi taimakon farko aka tafi shi zuwa wani asibiti a Katsina,” in ji majiyar.
Aminiya ta gano cewa maharan sun yi yunkurin sace wani ma’aikacin jinya ne da ke bakin aiki a lokacin, amma ya samu tserewa.
Sai dai an yi rashin sa’a ’yan fashin dajin sun yi awon gaba da matarsa, wadda ta biyo shi asibiti a lokacin.
“Ma’aikacin wucin gadi ne, ya zo ne za a yi wa wata mata tiyata, dama duk lokacin da yake aikin dare matarsa takan biyo shi, saboda tsoron zama ita kadai a gida.
“Wannan karon sai aka yi rashin sa’a ta fada a hannun ’yan fashin daji,” in ji shi.
Kafin yanzu garin Kurfi na cikin aminci, ’yan fashin daji ba su cika kai masa hari ba, sakamakon sintiri da ’yan banga ke yi, da kulawar mawadatan garin.
Daga bisani aka samu matsalar tsaro bayan rushewar ’yan banga, lamarin da wasu ke ɗora laifinsa a kan saɓanin siyasa tsakanin wasu manyan mutanen garin.
A kwanakin baya ma ’yan fashin daji sun yi garkuwa da wata uwa da ’ya’yanta tagwaye da kaninsu ɗan shekara hudu, a garin.
Wata majiya a Kurfi ta shaida wa wakilinmu cewa an sako matar da tagwayen nata bayan biyan kudin fansa miliyan N3.5.
Amma har yanzu ’yan ta’addan ba su sako yaron ba, suna nemans sai an ba su karin miliyan N1.5.
Wani ɗan garin na zargin tabarbarewar tsaron a kan baƙi da suka dawo Kurfi da zama a matsayin ’yan gudun hijira lokacin da garin ke zaune lafiya, suna ba wa masu ba ’yan ta’adda bayanai.
Shugaban Karamar Hukumar Kurfi, Mannir Shehu Wurma, ya tabbatar da harin, tare da cewa suna suna ɗaukar matakan kawo ƙarshen lamarin.