’Yan bindiga sun harbe wani direban bas suka sace mutane takwas da ke hanyarsu ta zuwa nadin sarautar Babban Limamin Bakarabonde a Masarautar Borgu a Jihar Neja.
Maharan suna kai farmakin ne a tsakanin yankunan Luma da Babanna da ke Karamar Hukumar Borgu a ranar Asabar.
- Dattawan Arewa sun bukaci a hukunta sojojin da suka kai harin bom a Kaduna
- Kotu ta daure matashi wata 6 kan satar magi da sabulu
Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar na neman Naira miliyan 17 a matsayin kudin fansar wadanda suka sace.
Wadanda lamarin ya rutsa da su ne kan hanyarsu ta zuwa nadin sarautar babban limamin Bakarabonde a masarautar Borgu.
Shugaban Karamar Hukumar Borgu, Alhaji Sulaiman Yerima, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana lamarin a matsayin abun takaici.
Ya kuma tabbatar da cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci Naira miliyan 17 a matsayin kudin fansa kafin sako fasinjojin.