Ana fargabar cewa wasu ’yan daban daji sun yi awon gaba da masallata kimanin arba’in, ciki har da mata da kananan yara daga wani masallaci a Unguwar Kwata da ke Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa, an sace masu bautar ne yayin da suke gabatar da sallar Tahajjudi, sallar tsakar dare da bisa al’ada aka saba gabatarwa a kwanaki goman karshe na watan Azumin Ramadana.
Aminiya ta ruwaito cewa, maharan sun yi wa masallacin dirar mikiya ne da misalin karfe biyu na dare, inda suka wawushe masallata 47 zuwa wani boyayyen wuri amma bakwai daga ciki sun samu nasarar tserewa daga hannunsu.
Wani mazaunin garin, Lawal Jibiya, ya ce mazauna kauyukan da ke makwabtaka da su tuni suka ankarar da su a kan yunkurin kawo harin na ’yan daban daji.
Akan haka ne daruruwan matasa da ’yan sa-kai suka yi shiri da zaman fakon maharan a hanyar shiga garin ta Daddara, Kukar Babangida da Magama.
Sai dai ya ce sun yi rashin sa’a a yayin da maharan suka tari hanzarinsu inda suka sauya hanya suka biyo ta wata hanyar daban kusa da Asibitin Yunusa Dantauri.
Ya kara da cewa, ’yan bindiga basu yi harbi ko sau daya ba har sai da suka gama tattare masallatan suka kama gabansu.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya tabbatar wa Aminiya da ingancin rahoton.
A cewarsa, “a jiya da misalin karfe 12 da rabi na dare su wadannan mahara suka zo dauke da muggan makamai inda suka tunkari shi wannan sabon masallacin da ke unguwar Abatuwa.
“Sabon masallaci yana nan a kan hanyar zuwa Madatsar ruwa ta Jibiya, inda akwai karancin zirga zirgar mutane wanda hakan ne ya bai wa ’yan bindigar damar kawo wannan hari.
“Sun tafi da mutane 40, amma Allah cikin ikon Sa lokacin da muka samu labari, ba tare da bata lokaci ba, jami’an tsaron suka bi sawun maharan kuma anyi nasarar ceto mutane 30 a lokacin.
“Sannan da safiyar yau, mun je don tantancewa a inda muka samu cewar mutane 10 ne a yanzu ba a san inda suke ba kuma muna ci gaba da bincike”, a cewar SP Gambo.